Honarabul Kayode Oladele mai wakiltar Imeko Afon/Egbado ta Arewa dake a Jihar Ogun ya bayyana cewa, kamataye Majalisar Dattawa ta kira tsohon shugaban hukumar hana almundahana, Nuhu Ribadu ba Lamorde ba.
Oladele ya bayyana cewa a lokacin da aka amso kudaden Nuhu Ribadu ne shugaban hukumar ba Lamorde ba. Sannan kuma ya bayyana cewa rashin tattaunawa da akayi akan kiran nashi a cikin majalisar ya nuna cewa ana so ayi ramuwa ne akan kiran da hukumar tayi ma matar shugaban Majalisar Dattawa, Saraki.
Oladele ya bayyana cewa idan aka kalli abun za’a ga cewa suna so su rama ne kawai. Yace:
“Idan ka kalli wanda ya kai karar, shi kanshi hukumar hana almundahana na bincikar shi. Kana mu sanya a ringa yi ma Majalisar Kasa dariya. Muna da tsarukan mu da dokoki. Kamar yadda nace a baya. Babu mai kare hukumar EFCC data ICPC. Amma idan za’ayi abu sai ayi shi yadda ya dace.
“Kun rika shi ne domin yazo yayi maku bayani akan abubuwan da yayi a lokacin da yake Daraktan aiyuka. Amma kun manta cewa shi ba shida cikakken ikon gudanar wa. Kuma baku kira tshon shugaban ba da tsohon Sakataren.
“Wannan ba komai bane illa ramuwa da suke so suyi. Kuna so wannan bawan Allah yazo ya baku bayanin da bai ma san shi ba.”
Note: There is a poll embedded within this post, please visit the site to participate in this post's poll.The post Binciken EFCC: Kamataye A Binciki Ribadu Ba Lamorde Ba – Honarabul Oladele appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read on NAIJ.COM.
Post A Comment:
0 comments:
We’re eager to see your comment. However, Please keep in mind that all comments are moderated according to our Comment Policy and all the links are nofollow. Using keywords in the name field area is forbidden.
Comment Using Either Disqus or Default Comment Mode.