Manyan Labarai Da Sukayi Fice A Ranar Talata

Share it:

Naij.com ta tattara maku manyan labarai guda 11 wadanda sukayi fice a ranar Talata 8 ga watan Disamba. Ku duba domin ku same su.

1. Sojojin Najeriya Sun Kashe Yan Boko Haram A Pulka
Sojojin Najeriya sunyi nasarar kashe yan Boko Haram da yawa a waje da suke rugawa daga dajin Sambisa.

2. Yan Najeriya Sunyi Zanga Zanga Akan Kudurin Dokar Shafukan Sada Zumunta
Yan Najeriya masu amfani da shafukan sada zumunta sunyi zanga zanga inda suka bukaci a fasa yin dokar. Sanata Bala Na’Allah ne na jihar Kebbi ya kawo kudurin. Masu zanga zangar suna rige da takardu masu rubutun #SayNoToSocialMediaBill

3. Sakataren Jam’iyyar LP Yayi Murabus
Sakataren jam’iyyar LP, Olukahode Ajalo yayi murabus. A wata wasika da ya aika ma shugaban jam’iyyar, Ajalo ya bayyana cewa yana so me ya koma ya dukiyar akan harkokin shari’ar da yake yi.

4. Boko Haram Sun Kashe Malamai 350, Makarantu 512
Shugaban hukumar ilimin bai daya na jihar Borno, Shettima Bukar Kullima ya bayyana cewa yan Boko Haram sun kashe malamai 350, makarantu 512 da kuma kimanin azuzuwan karatu 1000.

5. Zaben Kogi: Faleke Ya Koma Majalisa
Kasa da a wanni 72 bayan da aka gama zaben Kogi, tsohon mataimakin mafi gayu dan halartar jam’iyyar APC, James Faleke ya koma majalisar jihar Legas, inda dama dan majalisa ne a can.

6. Kila Hawan Jini Ya Kama Buhari – Orji Uzor Kalu
Tsohon gwamnan jihar Abia, Orji Uzor Kalu, ya bayyana cewa kila hawan jini ya kama Shugaba Muhammadu Buhari daga hawan shi mulki saboda yanayin da yaga Najeriya a ciki. Ya bayyana cewa shi yayi imani Buhari zaya kawo canji.

7. Tsohon Shugaban Kasa Jonathan Yaci Wata Kyauta A Switzerland
Tsohon shugaban kasan Najeriya, Goodluck Jonathan, yaci kyauta a kasar Switzerland. Zasu karrama shi saboda zaben 2015 daya gudanar da kuma kare hakkin bil Adama.

8. Za kayi Matakin Gidan Shugabar Mata Ta Jam’iyyar APC
Hajiya Ranatu Tijjani Aliyu itace shugabar mata ta Jam’iyyar APC. Sannan kuma itace shugabar kungiyar Jam’iyyun Afirika ta mata. Kwanakin baya tayi Wani hatsarin mota babba. Ta gayyaci Naij.com zuwa gidan ta a ranar Talata 8 ga watan Disamba.

9. Hotunan Matar Sarkin Ife Adeyeye
Tun bayan zabar shi Sarkin Ife, hotunan sabuwar sarauniyar Ife Olori Adebisi Adebukola Ogunwusi.

10. Shugaban Kasa Muhammadu Buhari Ya Karbi Ziyarar Shugaba Boni Yayi Na Jamhuriyar Benin
A jiya ne Shugaban kasan Najeriya Muhammadu Buhari, ya karbi ziyarar Shugaban kasar Benin, Boni Yayi, a fadar Shugaban kasan Najeriya dake Abuja.

11. Abun Dariya: Yadda Yan Sanda Italiya Suka Wulakanta Jaruman Nollywood Aki Da PawPaw
Kowane jarumi da Jarumi yana da nashi kalubalen. Kalubalen da Chinesu Ikedueze (Aki) da Osita Iheme (PawPaw) suka fuskanta shine, Wani Dan sanda Yayi barazanar Kama Wanda ya sanya su cikin mota ba tare da an sanya su cikin abunda ake sanya yara ba.

The post Manyan Labarai Da Sukayi Fice A Ranar Talata appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read on NAIJ.COM.

loading...
Share it:

Latest Stories

Post A Comment:

0 comments:

We’re eager to see your comment. However, Please keep in mind that all comments are moderated according to our Comment Policy and all the links are nofollow. Using keywords in the name field area is forbidden.
Comment Using Either Disqus or Default Comment Mode.