PDP: Kotu ta dakatar da Sheriff ta kuma umurci Makarfi da bari matsayin Ciyaman

Share it:

Babban kotun dake garin Fatakwal, wani babban birnin jihar Rivers, ta dakatar da Ali Modu Shariff tare da Farfesa Adewale Oladipo daga daukan kansu a matsayin jami’an Kwamitin jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) na kasa karkashin jagorancin Ahmad Makarfi a matsayin Ciyaman wata jam’iyya.

An samu goyon bayan kotun tare da umurni ga hukumar zabe da ta lura.

Babban kotu a garin port Harcourt ta bada umurnin wucin gadi na hana tsohon ciaman na PDP, Sanata Ali Modu Sheriff da Farfesa Adewale Oladipo wanda aka cire daga kujeran PDP a gurin zama ta al’ada da akayi a ranar Asabar 21 ga watan Mayu, 2016, ta hanesu da daukan kansu a matsayin jami’an wannan jam’iyya.

KU KARANTA KUMA:

Sakamakon korafi da ta taso daga jam’iyyar ta PDP, kotu ta kuma ba da umurnin hana bayar da sunayen duk wanda ta dakatar a matsayin jami’i ko dan takara zuwa ga hukumar zabe (INEC) daga lokacin da ta sanar kuma ta tabbatar da dakatarwan

matsayin ciyaman

Shugaban Jam’iyyar PDP Sanata Ali Modu Sheriff wanda yana da kara a gaban kotun

Bugu da kari, kotu ta bawa hukumar zabe ta kasa (INEC) daman kin amincewa da Sanata Alimodu Sheriff , Farfesa Adewale Oladipo da dukkanin jami’an da aka dakatar daga Kwamitin jam’iyyar PDP a garin Fatakwal.

Mai rikon Kwamitin jam’iyyar PDP na kasa Sanata Ahmad Makarfi, tsohon gwamnan jihar Kaduna, ya samu goyon bayan kotun tare da umurni ga hukumar zabe da su lura da dukkan alamura dangane da gudanar da zabe na farko domin ofish din siyasa, da kuma duba sunayen yan takara na ko wani zabe da hukumar INEC zata gabatar.

Da wadannan umarnin, za’a magance duk wani rikici a cikin jam’iyyar PDP

The post PDP: Kotu ta dakatar da Sheriff ta kuma umurci Makarfi da bari matsayin Ciyaman appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Nigerian newspapers | Read on NAIJ.COM.

loading...
Share it:

Latest Stories

No Related Post Found

Post A Comment:

0 comments:

We’re eager to see your comment. However, Please keep in mind that all comments are moderated according to our Comment Policy and all the links are nofollow. Using keywords in the name field area is forbidden.
Comment Using Either Disqus or Default Comment Mode.

Also Read

Supreme Court affirms election of four governors

  The Supreme Court on Wednesday upheld the elections of governors of four states across the federation. T

DR