Sarkin Kano ya nemi a kafa dokar auren Mace mai shekarau 18

Share it:

– Sarkin Kano yayi kira da a kafa doka don hana auren mata kasa da shekaru 18

– Sanusi ya nemi Najeriya tayi koyi da Misra da Morocco wajen bin addinin musulunci

Sarkin Kano Muhmammadu Sanusi na Biyu

Sarkin Kano Muhmammadu Sanusi na Biyu

Sarkin Kano Muhammadu Sanusi yayi kira ga al’ummar musulmin Najeriya dasu amshi canjin yanayi da suka samu kansu a halin yanzu sannan kuma su kauce ma auren yara yan kasa da shekaru 18.

Sarkin ya bayyana cewa lokacin da iyaye zasu bada diyar su aure sai a jira sai ta balaga sannan a kaita gidan miji ya wuce domin hakan ke kawo da mutuwar aure. Jaridar Preium Times ta bayyana cewa Sarkin ya fadi hakanne a taron Northern islamic Front.

Sarkin ya bayyana cewa ada mutane, Talaka da mai kudi duka suna auren mata 4 inda suke haihuwar Ya’ya 20 zuwa 30 saboda akwai arziki kuma mutane basu dogara da Gwamnati ba. Sarki Sanusi ya bayyana cewa hakan a yanzu ba zaya yiyu ba.

Ya bayyana cewa haihuwar yara da yawa yanzu ke sanya wasu iyayen su kasa ciyar da yaran sau 2 a ran. Ya kuma bayyana cewa akwai bukatar a kada doka da zata hana auren kananen yara.

Yace ” A misra a yanzu, shekarun auren mace akalla sai ya kai 18. Sannan a Malaysia da Morocco shekarun 19 ne da 18.

Sarkin ya nemi al’ummar musulmin da suyi koyi da wadannan kasashen Musulman da suka rigaya suka sanya wannan doka.

Sarkin ya bayyana cewa dukkanin wadannan kasashe mabiya koyawar Maliki ne don haka ya kamata Najeriya tayi koyi dasu.

Ya kuma bayyana cewa mafi yawan yara wadanda iyayen su basu daukar nauyin su yadda ya kamata ba wai kawai suna koyon munanen halaye bane ba, suna koyon ta’addanci da sauran abubuwan ashsha.

A wani labarin kuma, Wata mata ta karya dan kishiyar ta sau 8 inda ta yanke mashi harshe, ta kwakwule mashi ido kuma ta cire mashi ya’yan maraina.

The post Sarkin Kano ya nemi a kafa dokar auren Mace mai shekarau 18 appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Nigerian newspapers | Read on NAIJ.COM.

loading...
Share it:

Latest Stories

No Related Post Found

Post A Comment:

0 comments:

We’re eager to see your comment. However, Please keep in mind that all comments are moderated according to our Comment Policy and all the links are nofollow. Using keywords in the name field area is forbidden.
Comment Using Either Disqus or Default Comment Mode.

Also Read

BBNaija ‘Double Wahala’: Show sponsors displeased as CeeC alters dress, insults dressmaker

Housemates are usually provided clothes for the parties in line with each party theme. The post BBNaija ‘Double Wahala’:

DR