Ku bar Mata Musulmi su sanya Hijabi – Fafaroma

Share it:

Fafaroma Farncis, shugaban Kiristoci mabiya darikar Katolika na duniya, yayi kira ga mahukunta na kasar Faransa dasu bar mata Musulmi su sanya Hijabi kamar yadda Mata Kirista ke sanya Kuross da abubuwan da suka ga dama.

13895520_996999600398470_6152135321597517715_n

Fafaroma ya bayyana wannan ne bayan takunkumin da kasar ta sanya akan sanya Hijabi a cikin mutane. Wasu Bidiyoyi da suka fito kwanakin baya na nuna yadda yan sandan kasar ke musguna ma Mata musulmi idan suka fito da Hijabin su.

Fafaroma Francis ya kuma yi Allah wadai da batun gina katanka domin hana bakin haure shiga wasu kasashe kamar su Amurka. Fafaroma kuma ya soki kudin dan takarar shugabancin kasar Amurka, Donald Trump akan sanya kasar Mexico ta gina katanga domin hana mutanen kasar daga shigowa kasar Amurka din idan yayi nasarar lashe zaben.

The post Ku bar Mata Musulmi su sanya Hijabi – Fafaroma appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Nigerian newspapers 24/7.

loading...
Share it:

Latest Stories

Post A Comment:

0 comments:

We’re eager to see your comment. However, Please keep in mind that all comments are moderated according to our Comment Policy and all the links are nofollow. Using keywords in the name field area is forbidden.
Comment Using Either Disqus or Default Comment Mode.