Ga wasu muhimman labaran da Naij.com ta kawo muku a ranar Juma’a 27 ga watan Agusta
Buhari ya sake fita waje
Shugaba Muhammadu Buhari ya tashi daga filin jirgin saman Nnamdi Azikiwe a Abuja domin zuwa kasar Kenya a ranar Juma’a 26 ga watan Agusta.
KU KARANTA: Direba ya haddasa cunkoso saboda Sallah
Labari da dumi-dumi: Gwamna Bello na Kogi ya sha ruwan duwatsu
Rahotanni na cewa an jefi gwamma Yahaya Bello na jihar Kogi jim kadan bayan Sallar Juma’a a Lokoja.
Gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello
Sabbin wurare 6 da Buhari ke neman mai a Nigeria
Dakta Maikanti Baru shugaban Kamfanin Mai na kasar NNPC, ya bayyana sabbin wurare 6 da shugaban kasa ya bayar da umarni da a binciko Mai.
KU KARANTA: Dakunan manyan bakin EFCC a Abuja (Hotuna)
Karanta tanadin da rundunar soji ke yi wa tsagerun Niger Delta
Rundunar sojin Nigeria ta fitar da wasu hotuna na shirin dakarunta na tunkarar tsagerun Niger Delta a wani shirin da ta yi wa lakabi da “Murmushin kada” a yankin Niger Delta.
Sakatariyar Isoko da ake zargin matasa sun Bam
Wasu matasa sun tada bam a sakatariya
Rahotanni na cewa an ji karar tashi wasu abubuwan fashewa a Sakatariyar kungiyar ci gaban Isoko a garin Oleh da ke jihar Delta.
Matsin tattalin arziki: ‘Yan Nigeria na burin dawowar Jonathan
Sakamakon matsin tattlin arzikin da ‘yan Nigeria ke ciki, an bayar da rahoton cewa, wai, ‘yan kasar na fatan ganin dawowar Jonathan. An yi kiyasin cewa, a zamaninsa an sace biliyoyin nairori, baya ga hasarar rayuka da miliyoyin ‘yan gudun hijira da ake zargin ya haddasa a sakamakon rashin tabuka komai kan ‘yan Boko Haram.
The post Bitar wasu muhimman labaran Naij.com na ranar Juma’a appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read Naij.com 24/7.
Post A Comment:
0 comments:
We’re eager to see your comment. However, Please keep in mind that all comments are moderated according to our Comment Policy and all the links are nofollow. Using keywords in the name field area is forbidden.
Comment Using Either Disqus or Default Comment Mode.