– Wani masanin harkar tsaro, Onah Ekhomu, ya kira Gwamnati da ta ji tsoron sabon shugabancin Kungiyar Boko Haram.
– Ya zama dole, Jami’an tsaro, Rundunar Soji, Masu leken asiri, da sauran hukuma su zama cikin kintsi.
– Nadin sabon Shugaban Kungiyar ya nuna cewa akwai dangantaka sosai tsakanin Kungiyar ta Boko Haram da ISIS.
Nada Sheikh Abu Musab Al-Barnawi matsayin sabon Shugaba na Kungiyar Boko Haram ba abin wasa ba ne, musamman wajen fada da ta’addanci inji wata Kungiya mai suna AISSSON (Association of Industrial Security and Safety Operators of Nigeria). Jaridar Vangaurd ta rahoto cewa Shugaban AISSSON, Dakta Onah Ekhomu ya bayyna cewa dole Gwamnati ta dubi nadin sabon Shugaban Kungiyar Boko Haram a matsayin barazana daga ISIS. Dakta Onah ya kira mutanen kasa; Jami’an tsaro da sauran jama’a ka da su zama masu sakaci. Shugaban na Kungiyar AISSSON yace wannan ya tabbatar da cewa akwai alaka mai girman gaske tsakanin Kungiyoyin biyu; na Boko Haram da ISIS. Idan har ISIS za ta nada Shugaba a Najeriya, hakan na nufin Kungiyar ta na da hannu cikin harkar yan ta’addar a cikin Kasar nan. Yace ba mamaki Shugaban ISIS, Sheikh Abu Bakr El-Baghdadi ne da kan sa ya nada Sheikh Al-Barnawi.
KU KARANTA: YAN TAADAN BOKO HARAM SUN ARCE-SOJIN NAJERIYA
Boko Haram dai ta kashe mutane fiye da 30, 000 karkashin shugabancin Abubakar Shekau. Dr, Onah Ekhomu ya kira Sojin Najeriya da su zama cikin shiri da kintsi a ko yaushe. Dr. Onah yana ganin cewa Yan Boko Haram na kara shiri ne ba mika hannu ba kamar yadda ake dauka, ko yaushe kuma za su iya bada mamaki, kamar dai yadda aka san ISIS. Masanin harkar tsaron yace a guju sakin tubabbun yan ta’addan, wannan na nufin za su koma fagen daga ne bayan dan lokaci.
The post Boko Haram: Nadin Al-Barnawi abin tsoro ne-Inji wani Masanin tsaro appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read Naij.com 24/7.
Post A Comment:
0 comments:
We’re eager to see your comment. However, Please keep in mind that all comments are moderated according to our Comment Policy and all the links are nofollow. Using keywords in the name field area is forbidden.
Comment Using Either Disqus or Default Comment Mode.