Gernot Rohr ne sabon Kocin Super Eagles na Najeriya

Share it:

 

Hukumar kwallon kafa ta Najeriya NFF, ta zabi Bajamusen Kocin nan Gernit Rohr a matsayin sabon mai horas da yan wasan Super Eagles na Kasar.

Gernot Rohr tsohon dan wasan Kwallon Kafa ne

Shugaban Hukumar NFF ta Kasar, ya bayyana wannan labari, Mista Rohr na nam isowa zuwa Kasar a ranar Asabar.

Rohr ns Super Eagles

 

 

 

 

 

 

Hukumar kwallon kafa ta Kasar Najeriya watau NFF, ta zabi Bajamusen Kocin nan kuma tsohon dan wasan kwallon kafa, Gernit Rohr a matsayin sabon mai horas da yan wasan kwallon kafar Super Eagles na Kasar. Shugaban Hukumar kwallon kafar Kasar (NFF) ya bada wannan bayani, sabon Kocin zai iso Najeriyar domin ya fara aiki ne a ranar Asabar. Rohr zai zo Legas inda zai kalli wasan NPFL da za a buga tsakanin Kungiyar Ikorodu United da ta Sunshine Stars. A ranar Litinin kma zai wuce Abuja, inda za a bayyana shi ga idon duniya a matsayin sabon Kocin Super Eagles na Kasar.

KU KARANTA: INA NAN A NAN – INJI JOHN MIKEL OBI

Shugaban Hukumar NFF ta Najeriya, Amaju Pinnick yake cewa, ana shirin kammala yan abubuwan da ba za a rasa bane da suka rage, don tun tuni aka fara maganar dauka hayar Kocin, an dai dakatar da sanar da jama’a ne har sai komai ya tabbata. Rohr Gernit dai tsohon dan wasan kwallon kafa ne, kuma asalin sa mutumin Kasar Jamus ne. Yanzu haka yana aiki da Kungiyar Kwallon Kafa ta Kasar Jamus (DFB) din.

A bara dai, Kasar Burkina Faso ta sallame sa daga aikin horar da yan kwallon Kasar, an kuma saka sunan sa cikin wadanda za su karbi aikin horar da yan kwallon Kasar Guinea a watan Jiya.

 

 

The post Gernot Rohr ne sabon Kocin Super Eagles na Najeriya appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read Naij.com 24/7.

loading...
Share it:

Latest Stories

Post A Comment:

0 comments:

We’re eager to see your comment. However, Please keep in mind that all comments are moderated according to our Comment Policy and all the links are nofollow. Using keywords in the name field area is forbidden.
Comment Using Either Disqus or Default Comment Mode.