Wasan Kofin ‘Community Shield’: Ya za ta kaya tsakanin Man Utd da Leicester City?
Kungiyar Manchester United za ta fafata da Kungiyar Leicester City a wasan cin kofin ‘Community Shield’ na Ingila a ranar Lahadin nan, 7 ga watan Agusta, a babban filin wasa na Wembley. Man Utd dai ta nada sabon Koci Jose Mourinho, bayan ta dauki kofin FA, Kungiyar Leicester kuwa ta ba duniya mamaki, inda ta dauki kofin Premier League.
Kungiyoyin duka sun yi sababbin sayayya domin kara karfi, Man Utd sun kawo yan wasa irin su Henrikh Mkhitaryan, Zlatan Ibrahimovic. Kungiyar Leicester kuwa ta sayo Ahmed Musa na Najeriya da wasu dabam. To ko ya za gwabza idan wadannan Kungiyoyi sun hadu?
KU KARANTA: YA KAMATA A DAURE KOCIN MANUTD, JOSE MOURINHO INJI WANI LAUYA
1. Wasan Zlatan Ibrahimovic da Henrikh Mkhitaryan na farko:
Ba shakka, za a take da sababbin yan wasan biyu a wasan na gobe. Zlatan Ibrahimovic zai buga sama lamba tara, da kuma Wayne Rooney a bayan sa, sannan kuma ga Henrikh Mkhitaryan a barayin dama, da Antonio Martial a bangaren hagu.
2. Ahmed Musa a gaban Leicester City:
A cikin wasannin yada zangon da Kungiyar ta Leicester City ta buga, Ahmed Musa ne abin maganar, inda ya buga gefen Jamie Vardy. Claudio Ranieri zai yi amfani da yan wasan biyu masu gudun tsiya a wasan.
3. Yan wasan Man Utd:
Yawancin yan wasan Kungiyar Man Utd na son ganin sun burge sabon Kocin nasu, domin su sami wuri a Kungiyar, wannan zai sa duk su dage wajen fito da kan su a wasan. Musamman yan wasa irin su Memphis Depay.
4. Sabon tsarin wasa:
Man Utd ta buga tsarin kwallo na 4-3-3 wancan shekarar, haka kuma Leicester tayi amfani da 4-4-1-1, amma ganin kowa ya sayo sababbin yan kwallo, ana tunanin za a ga sabon tsarin buga wasa. Ana tunanin mai Leicester zai koma buga 4-3-3 saboda zuwan Ahmed Musa, Jose kuma na Man Utd zai yi amfani da 4-4-1-1 ko 4-4-2; da Zlatan Ibrahimovic tare da Rooney a bayan sa.
5. Wasan ‘taho-mu-zuba’ na Leicester:
Kowa ya san Leicester City da kwallon tsinkewa da zurawa a guje, duk da zuwan sabbabin yan wasa, Kungiyar za tayi kokarin amfani da wannan dabara na ta na zurawa a guje idan an samu sarari, musamman ganin ga Ahmed Musa da Jamie Vardy.
The post Kofin Community Shield: Tsakanin Man Utd da Leicester? appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read Naij.com 24/7.
Post A Comment:
0 comments:
We’re eager to see your comment. However, Please keep in mind that all comments are moderated according to our Comment Policy and all the links are nofollow. Using keywords in the name field area is forbidden.
Comment Using Either Disqus or Default Comment Mode.