Zaben PDP: Dokpesi da Bode George sun kudiri niyya

Share it:

 

– Raymond Dokpesi yace bai yarda da yarjejeniyar mika kujerar Shugabancin Jam’iyyar PDP zuwa wani bangaren Kasar ba.

– Shi kuwa Bode George cewa yake, ba abin da Jam’iyyar PDP ta ke nema yanzu irin wanda ya ga jiya, ya ga yau.

– George ya bayyana cewa idan dai har ana son a ga an gyara Jam’iyyar PDP, to a zabe sa.

PDP Dokpesi

 

 

 

 

 

 

 

 

 

Manyan jiga-jigai na PDP; Raymond Dokpesi da Bode George sun yanki takardar tsayawa takarar Shugabancin Jam’iyyar ta PDP. Sai dai Dokpesi zai fuskanci matsala guda, ‘ya ‘yan Jam’iyyar PDP na yankin kudancin Kasar sun mika kujerar zuwa ga ‘yan bangaren Kudu-maso-yammacin Kasar, an yanke wannan shawara ne a wani taro na masu ruwa da tsaki a Garin Fatakwal a ranar Alhamis. Mutane 89 cikin 92 na ‘ya ‘yan Jam’iyyar PDP suka amince da a mika kujerar ga yankin Kudu-maso-Yammar Kasar. Dan takara Raymond Dokpesi yace shi babu ruwan sa da wannan tsari, kuma sai ya tsaya takarar sa. Shi kuwa Bode Geroge, wanda shi ma ya karbi takardar tsayawa takara kujerar Shugabancin Jam’iyyar, yace yana da shirin shawo kan matsalolin da PDP ta ke fuskanta.

KU KARANTA: PDP TA SAMU MILIYAN SHIDA DALILIN IYE-IZEAMU A EDO

Bode George yana mai bayyana cewa, ba abin da  Jam’iyyar PDP ta ke nema a wannan hali illa mutumin da ya ga jiya, kuma ya ga yau. Bode George yace shi fa rikakken dan Jam’iyya ne, bai taba barin ta ba ko da wasa, kuma ba ya tsoron dan kowa, don haka ya cancanta a zabe sa. Kuma ya rike makamen; Mataimakin Shugaban  Jam’iyyar PDP (Kudu ta Yamma), Mataimakin Shugaban  Jam’iyyar PDP (Kudancin Najeriya), Mataimakin  Jam’iyyar PDP (Na Kasa) baki daya. Saboda haka idan har aka zabe sa, zai gyara Jam’iyyar PDP mai adawa a Kasar.

 

The post Zaben PDP: Dokpesi da Bode George sun kudiri niyya appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read Naij.com 24/7.

loading...
Share it:

Latest Stories

Post A Comment:

0 comments:

We’re eager to see your comment. However, Please keep in mind that all comments are moderated according to our Comment Policy and all the links are nofollow. Using keywords in the name field area is forbidden.
Comment Using Either Disqus or Default Comment Mode.