Abin bakin ciki! Sa’o’i 24 bayan rantsarwa, karanata abunda ya faru da wannan matar (Hoto)

Share it:

An rahoto cewa wata mata ta mutu haka kawai sa’o’I 24 bayan an rantsar da ita a matsayin sakatariya

An rahoto cewa Mrs Olubunmi Odumusi ta mutu, haka kawai sa’o’I 24 bayan an rantsar da ita a matsayin sakatariya a jihar Ogun. A cewar ahlin gidanta, tayi bacci ne wanda daga nan bata kuma tashi ba sai gawar ta.

Yar jaridar mai shekaru 57 tana ganin Likita a kasar Amurka ida take karban maganin cutar daji, an rahoto cewa ta dawo kasar a lokacin da taji labarin matsayin da aka bata, harma ta hallaci taron a kan wani keken guragu a ranar Alhamis, 1 ga watan Satumba.

Olubunmi Odumusi

Marigayiya sakatariyar jihar Ogun

Tsohon gwamnan jihar, Gbenga Daniel wanda yayi aiki da marigayiya Odumusi, ya fadi wannan:

“Na taya sauran mutane cikin jimami tare da yan uwan Mrs Olubunbi Odumusi. Ina tunawa da ita a matsayin daya daga cikin daraktoci masu himma da kwazo, wadanda suka taimaka a gwamnatinmu tunda farko.

KU KARANTA KUMA: Jihar Sakwato ta fitar da dalibai 39 daga jami’o’in kasar waje

“Ta taimaka sosai a gurin tsara yankunan jihar wanda mukayi kuma tana daya daga cikin mayan magoya bayan shirin. babu shakka Gwamnatin jihar Ogun tayi rashi mai tsanani kuma addu’ata gareta shine Allah yaji kanta da gafara ya kuma bay an uwanta ikon juriyar wannan baban rashi mai ciwo, a lokacin da ya kamata suyi murnar cigaban da ta samu.”

Allah ya ji kanta da gafara!

The post Abin bakin ciki! Sa’o’i 24 bayan rantsarwa, karanata abunda ya faru da wannan matar (Hoto) appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read Naij.com 24/7.

loading...
Share it:

Latest Stories

Post A Comment:

0 comments:

We’re eager to see your comment. However, Please keep in mind that all comments are moderated according to our Comment Policy and all the links are nofollow. Using keywords in the name field area is forbidden.
Comment Using Either Disqus or Default Comment Mode.