– Osaro Onaiwu yayi zargin magudi a zaben jihar Edo, da kuma dan takaran APGA yace ayi sabon lale, inda yace ba’ayi wani zaben hakika ba.
Dan takaraan gwamnan jihar Edo karkashin jam’iyyar APGA , Osaro Onaiwu,yayi kira da cewa ayi watsi da zaben da ake gudanar wa a jihar a yanzu.
Osaro Onaiwu yace: “Mutane sun fito kwansu da kwarkwatansu saboda suna son canji” kuma an mamaye zaben da cin hanci da rikici. PDP da APC sun hana mutane zabe. Wannan bas hi bane demokradiyyan da muka nema ba,wannan ba irin demokradiyyan da muke so ma yayanmu bane.
“Na nemi ayi watsi da zaben tun karfe 2 na rana saboda wannan zabe bogi ne. a inda nayi zabe, yan daban APC sun kwace akwatin zabe.”
KU KARANTA: Zaben jihar Edo: Ku duba sakamakon zabe daga hukuma
A bangare guda, Gwamna Nasir El-Rufai ya musanta zargin da dan takaran jam’iyyar PDP yake masa jawabin da ya bayar ta mai magana da yawunsa Samuel Aruwan yace:
“Malam Nasir El-Rufai bai je jihar Edo ba a jiya, Laraba 28 ga watan Satumba sabanin tatsuniyar da daya daga cikin yan takaran yayi a gidan Talabijin.”
Kana gwamna Adams Oshiomhole ya karyata maganan cewa gwamna Nasir El-Rufai ya je Jihar. Ya yi bayani ne saboda kawai a tabbatar da cewa karya ake yi, Duk da cewa doka bata hana kowani dan kasa ya je ko ina a cikin kasan ba.
The post Dan takaran APGA yace anyi magudi a zaben jihar Edo appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read Naij.com 24/7.
Post A Comment:
0 comments:
We’re eager to see your comment. However, Please keep in mind that all comments are moderated according to our Comment Policy and all the links are nofollow. Using keywords in the name field area is forbidden.
Comment Using Either Disqus or Default Comment Mode.