Hukumar yaki da zamba da yima tattalin arzikin kasa zagon kasa EFCC ta kammala shirin gurfanar da Femi Fani-Kayode kan laifin satan kudade a ranar Alhamis 10 ga watan Nuwamba.
Kaakakin hukumar EFCC Wilson Uwujaren ya bayyana ma kamfanin dillancin labarai (NAN) haka ta hanyar sakon kart a kwana a ranar Talata 25 ga watan Oktoba daga Abuja. Uwujaren yace hukumar ta aika ma tsohon ministan sammaci, sai dai bai yi karin bayani ba.
Dama can hukumar ta shigar da Femi Fani Kayode tare da Nenadi Usman gaban kuliya kan laifin cin hanci da rashawa. Ciki har da wani Danjuma Yusuf da kamfanin Joint Trust Dimension Nigeria LTD.
Hukumar na tuhumarsu ne da aikata laifuka 17, dasu ka hada da satan kudi, biyan kudi ba’a kan ka’ida ba tare da kashe kudi ba’a kan ka’ida ba da suka kai naira biliyan 4.9, sai dai duk musanta laifukan.
Rahotanni sun bayyana cewa lauyan gwamnati Rotimi Jacob ya shaida ma kotu shedunsa, inda aka dage karan zuwa ranakun 14 da 15 ga watan Nuwamba don cigaba da shari’an.
KU KARANTA: Hotunan Janet Jackson dauke da juna biyu, sanye da Hijabi,
Shi dai Femi Fani Kayode ya taba zama tsohon daraktan watsa labarai na kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa Jonathan, an sake kamashi yayin da yake fitowa daga babban kotun tarayya a ranar juma’a 21 ga watan Oktoba. A daidai lokacin da yake kan hanyar fita ne wasu jami’an hukumar EFCC suka raka shi zuwa motar su dake jiransa.
Tun lokacin ne Femi Fani Kayode ke hannun hukumar. A wani labarin kuma, hukumar EFCC ta musanta batun da ake yayatawa na cewa wai tsohon ministan ya yanke jiki ya fadi a farfajiyarsu. Kaakakin hukumar Uwujaren yace babu kamshin gaskiya a cikin batun.
The post EFCC ta sanya ranar gurfanar da Fani-Kayode gaban kuliya appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read Naij.com 24/7.
Post A Comment:
0 comments:
We’re eager to see your comment. However, Please keep in mind that all comments are moderated according to our Comment Policy and all the links are nofollow. Using keywords in the name field area is forbidden.
Comment Using Either Disqus or Default Comment Mode.