Femi Fani-Kayode ya sume a dakin kurkukun EFCC

Share it:

– Tsohon ministan sufurin jirgin sama, Femi Fani-Kayode,ya sume warwas a dakin kurkukun hukumar EFCC

– Rahotanni sun nuna cewa ya sume ne a arannan Asabar, 22 ga watan Oktoba

– Amma an samu likitan hukumar wanda ya kawo agaji na gaggawa

EFCC arrests Fani Kayode

Fani Kayode

An samu rahotan cewa tsohon ministan sufurin jirgin sama, Femi Fani-Kayode, ya sume a dakin kurkukun hukumar hana almundahana da yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa wato EFCC.

Mai Magana da yawun Femi Fani-Kayode, Jude Ndukwe yace mai gidansa ya sume ne a ranan asarbar 22 ga watan oktoba amma likitocin hukumar su bayar da agaji na gaggawa.

KU KARANTA: Bayan wata daya da barin “Kitchen da dayan dakin,” Aisha Buhari ta dawo Najeriya (Hotuna)

Yayi da yake yabawa likitocin EFCC, Jude Ndukwe,ya bayyana cewa an dade da fadawa hukumar yanayin lafiyansa bayan sun tsare na tsawon kwanaki 67.

An damke Fani Kayode a karon farko ne a ranan 9 ga watan Mayu, bayan ya kai kansa ofishin hukumar akan gayytar da suka masa na almundanahan kudin yakin neman zaben jam’iyyar PDP a 2015.

Sun gurfana a kotu tare tsohuwar minister, Nenadi Usman tare wasu guda 2. Daga baya aka sake shi aranan 15 ga watan Yuli bayan sun biya belin babban kotun tarayya mai zaune a kegas ta bayar.

Kana kuma an sake damke a ranan juma’a 21 ga watan Oktoba,bayan ya gurfana a kotu.

The post Femi Fani-Kayode ya sume a dakin kurkukun EFCC appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read Naij.com 24/7.

loading...
Share it:

Latest Stories

Post A Comment:

0 comments:

We’re eager to see your comment. However, Please keep in mind that all comments are moderated according to our Comment Policy and all the links are nofollow. Using keywords in the name field area is forbidden.
Comment Using Either Disqus or Default Comment Mode.