– Ibrahim Magu, shugaban hukumar hana almundahana yace duk ma’aikacin gwamnati yana kalkashin bincike
– Magu, yace yana da umurnin shugaba Muhammadu Buhari na ya binciki duk dan Najeriya wanda ke da abin bincike komin alakarsa ta siyasa
– Shugaban hukumar hana almundahanar ya kira cin hanci a matsayin laifi ga bil adama
Ibrahim Magu, shugaban hukumar hana almundahana da yima tattalin arzikin kasa zagon kasa (EFCC) yace kowane ma’aikacin gwamnati na kalkashin bincike ba tare da saninsa ba. Yayi watsi da zargin da ake ma EFCC cewa binciken nata na bangare daya ne.
KU KARANTA:EFCC ta sanya ranar gurfanar da Fani-Kayode gaban kuliya
Ya cigaba da cewa: “muna da dalilan bincike,kuma muna bincikar ma’aikatan gwamnat ba tare da saninsu ba”,
Shugaban hukumar hana almundahanar ya ambaci haka lokacin da ya kai ziyarar ban girma a helkwatar kungiyar ma’aikatan masaku, madinka da teloli (NUTGTWN) a Kaduna ranar Talata 25 ga Oktoba inda ya kira cin hanci a matsayin laifi ga bil adama.
The post Ina da umurnin bincikar kowa da kowa – Shugaban EFCC appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read Naij.com 24/7.
Post A Comment:
0 comments:
We’re eager to see your comment. However, Please keep in mind that all comments are moderated according to our Comment Policy and all the links are nofollow. Using keywords in the name field area is forbidden.
Comment Using Either Disqus or Default Comment Mode.