Wani alkalin kotun majistri ya kama daure shugaban karamar hukumar Buruku ta jihar Benuwe mai suna David Yiman.
David Yiman shine sabon shugaban hukumar da gwamnan jihar Samuel Ortom ya nada a ranar 11 ga watan Oktoba, an daure shi tare da Kosuvenyi Kungwa da Emmanuel Nyajo kan zarginsu da aikata laifin kisan kai.
Yansanda sun kama mutanen uku ne kan zarginsu da kisan wani malamin jami’ar Mkar Aondosso Wilfred mai shekaru 50 wanda jaridar Punch ta ruwaito cewa an kashe malamin ne a watan Agusta 2016. Ana zargin mutanen ne da hadin baki tare da wasu mutane uku wajen yin kisan.
KU KARANTA: Mata sun yi garkuwa da sakataren gwamnatin jihar Delta
Sai dai a zaman kotun na farko, ba’a saurari korafin da wasu suka shigar na kalubalantar hurumin alkalin na sauraren karar. Lauyan hukumar yansanda Hyacenth Mbakwor yace haryanzu ba’a kammala binciken lamarin ba. Daga nan sai ya bukaci kotu da ta dage sauraron karar zuwa wani rana na daban.
The post Kotu ta daure shugaban karamar hukuma a gidan yari appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read Naij.com 24/7.
Post A Comment:
0 comments:
We’re eager to see your comment. However, Please keep in mind that all comments are moderated according to our Comment Policy and all the links are nofollow. Using keywords in the name field area is forbidden.
Comment Using Either Disqus or Default Comment Mode.