Fitaccen tsohon dan wasan kungiyar Arsenal Thierry Henry ya shiga sahun gaba wajen kare dan wasan Manchester United Paul Pogba bayan ya sha suka daga wajen Gary Neville da mai horar dasu Jose Mourinho.
Yan wasan kungiyar Manchester, musamman Paul Pogba sun sha suka daga magoya bayan ta bayan sun sha kayi a hannu kungiyar Chelsea a ranar Lahadi. Shima Jose Mourinho bai ji da dadi ba a yayin da ya kai bakonci tsohuwar kungiyarsa.
Magoya bayan kungiyar sun bayyana bacin ransu da rashin tabuka komai “abin kunya ne ace Kante ya ratsa ta tsakanin Herrera da Pogba, abin haushin ma dukkaninsu yan wasa tsakiya ne.”
Shima Gary Neville yace “Manchester sun ta kashe pan miliyan 180 a siyan yan wasan tsakiya, amma har yanzu kwalliya bata biya kudin sabulu ba.” Inji Gary Neville.
KU KARANTA:Darajan Naira yayi cak a N455/$1 a kasuwannin bayan fagge
Idan ba’a manta ba shima Mourinho ya soki Pogba yanacewa “zatona shi ne idan Pogba na cikin fili, zamu samu daman fasa masu tsaron gidan Chelsea. Amma a fannin tsaron gida mun danyi kokari, sai dai muna bukatan sake zage damtse.”
Sai dai Thierry Henry yace “idan ana maganan Pogba ne, toh ya kai duk inda dan wasa ya kai. Nima lokacin da na zo Firimiya, ban tabuka wani abin kirki ba. Yan wasa dayawa basa fara kwallon kirki. Abin kadan kadan ake faraway, amma yanzu sai yan jaridu da magoya baya su hura ma dan wasa wuta.”
Henry ya cigaba da cewa “Pogba na bukatan lokaci. Duk mun san abinda zai iya yi, kuma ina da yakinin zai gyaru. Sai kuma shima Mourinho, yana da rawar da zai taka wajen duba inda zai yi amfani da shi. Abin dai ba sauki, shi kansa Mourinhon yanzu yazo”
The post Tsohon dan wasan Arsenal, Henry ya yaba ma Pogba appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read Naij.com 24/7.
Post A Comment:
0 comments:
We’re eager to see your comment. However, Please keep in mind that all comments are moderated according to our Comment Policy and all the links are nofollow. Using keywords in the name field area is forbidden.
Comment Using Either Disqus or Default Comment Mode.