Naij.com ta tattaramaku manyan labarai masu amfani Guda Tara wadanda suka faru a ranar Talata, Yuli 21. Sai ku duba domin samun su.
1. Tsohon Shugaban Jami’an tsaron Jonathan bai mutu ba.
Bayan da farko akace ya mutu, Gordon Obua tsohon Shugaban Jami’an tsaron tsohon shugaban kasa Jonathan ya fito da kansa ya karyata jita-jita cewa wai ya mutu.
2. Wani toshon Sanata a Bayelsa yace tilasta Jonathan akayi a kansu.
John Brambaifa yace Jam’iyyar Peoples Democratic party zata fadi zaben da za’ayi a Jihar Disamba 5 saboda Bakin Jinin tsohon Shugaban kasa Jonathan a Jihar.
3. Kuskuren da Obama yayi lokaci da yake magana akan Najeriya.
Zuwan shugaban Kasa Buhari Amurka ya samu karbuwa sosai kuma babban labari ne a Jiya.
4. Tsakanin zuwan Buhari da Jonathan Amurka.
Yan Najeriya na kokarin fayyacewa a tsakin zuwa Buhari Amurka dana Jonathan wasu Watanni kafin ya sauka.
5. Yan Arewa sun roki Dasuki kada yaje Kotu.
An Shawarci Sambo Dasuki tsohon mai bawa Shugaban Kasa Shawara akan Tsoro kada yaje ya kai karar Gwamnatin Tarayya Kotu, soboda hakan zai jawo tone-tonen asiri da alakar Yan Boko Haram da wasu Yan Arewa da Jam’iyyar APC.
6. AAG: Buhari ya amince fidda kudin wasannin Afirika Wata Biyu kafin a Fara.
Shugaba Buhari ya sha gaban tsohon Shugaban Kasa Jonathan inda ya amince a fidda kudin wasannin Afirika na 2015 da za’ayi Wata Biyu kafin lokacin.
7. Nafe-naden da Buhari yayi da kuma wadanda ya kora.
Kamar yadda yayi alkwari lokacin yakin neman zabe, shugaba Buhari yayi kokari wajen nada mutagen kirki da zasu taya shi aiki.
8. Boko Haram sun kai hari a Kyauyan su Shugaban Sojan Kasa.
Haramtacciyar kungiyar nan ta Boko Haram ta kaima Kyauyan Buratai dake cikin Karamar Hukumar Biu hari, inda ta kashe mutane da yawa kuma ta kone gidaje da yawa. Cikin gidajen harda na tsohon Kwamishina Barista Isa Buratai.
9. Christiane Amanpour ta CNN tayi hirar da Buhari.
A Daren Talata 21, Fitacciyar Mai rahotanin labaran kasashen waje Chiristiane Amanpour tayi hirar da Shugaba Buhari.
The post Manyan Labarai Guda Tara Da Suka Faru A Ranar Talata 21 Ga Watan Yuli appeared first on News on Naij.com | Today's Nigeria Breaking news & headlines..
Post A Comment:
0 comments:
We’re eager to see your comment. However, Please keep in mind that all comments are moderated according to our Comment Policy and all the links are nofollow. Using keywords in the name field area is forbidden.
Comment Using Either Disqus or Default Comment Mode.