Zaben Bayelsa: Patience Jonathan Ta Juya Ma Dickson Baya

Share it:

Jita-Jita a cikin jihar Bayelsa na cigaba da nuna cewa matar tsohon shugaban Najeriya, Patience Jonathan ta juya ma gwamnan Bayelsa mai ci yanzu, Seriake Dickson baya.

Patience-Jonathan

Matar tsohon shugaban kasa, Patience Jonathan

Sannan kuma wani rahoto ya nuna cewa patience tayi wata ganawa ta rufin asiri da Timipre Sylva a juhar Fatakwal a ranar Kirisimeti.

Nathan Egba, wanda shine mai hudda da jama’a na kungiyar yakin neman zabe Sylva ya bayyana cewa Sylva bai yi wani taro da tsofaffin tsagerun Nija Delta ba. Amma dai yayi shiru akan ganawar su da Patience Jonathan.

Patience Jonathan dai ta bada da Dickson da dadewa. Dattijan Bayelsa ne suka shirya su a ranar 2 ga watan Satumba inda aka tattauna tare da  tsihon gwamnan Jihar, Diepreye Alamieseigha.

Daga bisani ne Patience ta shawarvi magoya bayan ta suyi aiki tukuro domin cin nasarar Dickson. Rikicin nasu ya fara ne daga lokacin da Patience tayi murabus daga matsayin ta na babbar sakatariyar Jihar ta Bayelsa.

Na kusa da ita sun bayyana cewa tayi haka ne domin ta kaucema faduwa zaben PDP kada mijinta yaji kunya.

The post Zaben Bayelsa: Patience Jonathan Ta Juya Ma Dickson Baya appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read on NAIJ.COM.

loading...
Share it:

Latest Stories

Post A Comment:

0 comments:

We’re eager to see your comment. However, Please keep in mind that all comments are moderated according to our Comment Policy and all the links are nofollow. Using keywords in the name field area is forbidden.
Comment Using Either Disqus or Default Comment Mode.