Gasar Olympics: Mikel Obi ne kyaftin din Najeriya

Share it:

 

– John Mikel Obi ne Kyaftin din Kungiyar U-23 ta Najeriya a gasar Olympics da za a buga a Rio na Brazil.

– Kocin Kasar, Siasia yace abin ya zo da sauki, domin Mikel ne kyaftin din Kungiyar Super Eagles., saboda haka aka zabe sa ma a nan.

– Mikel yace ko dan wannan karamci da aka yi masa, dole Najeriya ta yi nasara a Kasar Brazil.

Mikel

 

 

 

 

 

Ko da dai abin ba zai yi ma wasu dadi ba, an nada dan wasan tsakiyar Chelsea John Mikel Obi a matsayin kyaftin din Kungiyar U-23 na Najeriya da za su wakilci Kasar a Gasar Olympics da za a gudanar a Birnin Rio da ke Brazil. Kocin Kungiyar, Samson Siasia mai shekaru 48 ya bayyana hakan a ranar Asabar 30 ga watan Jiya, Yuni a wani taro da manema labarai. Kocin ya bayyana cewa dan wasan ne kyaftin din Super Eagles na Kasar, saboda haka ba abin da ya dace sai a nada sa kyaftin din wannan kungiyar ta U-23.

KU KARANTA: KARANTA ABIN DA EGUOVEN YAKE CEWA

Siasia yace ai ba wani wata-wata, dole ne Mikel kawai zai zama kyaftin din sa. “Bayan na tattauna da dukkanin su biyu (Mikel da tsohon kyaftin din U-23 din) nayi masu bayani, kuma duk sun fahimta. Nayi murna da na ga cewa Azubuike (wanda shine kyaftin din mu a baya) ya gamsu da bayanan, ya kuma amince ya mikan kambun ga Mikel Obi.” Inji Kocin Kasar Siasia. Ya kara da cewa: “Ni ba karamin abin farin cika na bane ace na nada kyaftin da yake shine kyaftin a Kungiyar Super Eagles ta Kasa… Yan wasan kaf, sun yi mubaya’a ga Mikel Obi a matsayin sabon kyaftin din su”

Dan wasa Mikel ya nuna farin cikin sa da wannan abu, a baya dai dan wasa Okechukwu Azubuike ya rike ma Najeriyar kambu a duk wasannin da ta buga na zuwa Gasar ta Olympics. Mikel Obi yace dole fa Kasar ta samu yin nasara a wannan Gasa da za a buga a Garin Rio.

The post Gasar Olympics: Mikel Obi ne kyaftin din Najeriya appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Nigerian newspapers 24/7.

loading...
Share it:

Latest Stories

Post A Comment:

0 comments:

We’re eager to see your comment. However, Please keep in mind that all comments are moderated according to our Comment Policy and all the links are nofollow. Using keywords in the name field area is forbidden.
Comment Using Either Disqus or Default Comment Mode.