Hukumar JAMB ta janye jerin sunayen da ta tura Makarantu

Share it:

 

– Hukumar Jarabawar JAMB ta Najeriya, ta janye jerin sunayen da ta aika makarantun gaba da Sakandare na Kasar.

– Hukumar ta ba Makarantun Kasar hakuri game da wannan mataki da ta dauka.

– JAMB ta bayyana cewa, ko kusa kada dalibai su ta da hankalin su, domin hakan yana cikin tsare-tsaren wannan shekara ta 2016.

JAMB

Wasu dalibai yayin rubuta jarrabawar JAMB ta shiga makarantu na gaba da Sakandare

Hukumar JAMB ta Najeriya ta janye jeringiyar sunayen wadanda suka rubuta jarabawar daga manyan makarantun Kasar na gaba da Sakandare, bayan ta tura sunayen na su a baya. Shugaban da ke kula da yada labarai na Hukumar ta JAMB, Fabian Benjamin ya bayyana haka ga Jaridar Premium Times. Hukumar ta bayyana cewa anyi hakan ne domin tabbatar da bin dokar Kasa.

KU KARANTA: KU KYALE MATA SU SANYA HIJABI INJI FAFAROMA

Ga bayanin da JAMB tayi kamar haka:

An yi wannan ne don ganin tabbatar da cewa Jam’i’oi sun gudanar da aikin su na dibar dalibai kamar yadda ya dace. Bayan haka ne kuma, sai su aiko ma Hukumar JAMB daliban da suka dauka, kamar dai yadda Ministan Ilmi ya bada umarni a taron da aka yi. An tura jerin sunayen farko ne domin ganin tsarin ya tafi yadda ya dace ba tare da tangarda ba. Saboda haka, ka da wadanda suka rubuta jarrabawar su tada hankalin su, domin wannan duk yana cikin sabon tsarin da aka kawo na wannan shekara ta 2016. Hakazalika, Hukumar JAMB tana bada hakuri ga duk wani wanda aka matsa ma wa sanadiyar hakan.

Hukumar JAMB dai ta bayyana yadda za a bi a dauki dalibai zuwa Jami’a a baya, sai dai hakan bai yi ma Kungiyar ASUU ta malaman Jami’an dadi ba ko kadan, Kungiyar ta ASUU ta bayyana cewa JAMB ta na nema ta wuce gona da iri, domin kuwa ba hurumin ta ba ne wannan. ASUU ta bayyana cewa Jami’a ce ta ke da damar daukar daliban ta, bisa ka’idar ta.

 

The post Hukumar JAMB ta janye jerin sunayen da ta tura Makarantu appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Nigerian newspapers 24/7.

loading...
Share it:

Latest Stories

Post A Comment:

0 comments:

We’re eager to see your comment. However, Please keep in mind that all comments are moderated according to our Comment Policy and all the links are nofollow. Using keywords in the name field area is forbidden.
Comment Using Either Disqus or Default Comment Mode.