-Kakakin majalisar Wakilai Dogara da shugabannin majalisar sun lamkwame sama da Biliyan 10
-Abdulmumini Jibri ya sake magantuwa kan badakalar majalisar
-Halin da Najeriya ke cikin daga majalisar ne
Jibrin Kofa da Yakubu Dogara
Abdulmumini Jibrin ya zargi Kakakin Majalisar Wakilai Yakubu Dogara, da wasu manyan shugabannin Majalisar su 8 da lankwame sama da biliyan 10 a matsayin alawus-alawus a tsawon shekaru. Korarren shugaban kwamitin kasafin kudin Majalisar ya yi wannan zargin ne a ranar Juma’a 26 ga watan Agusta, a cewar jaridar Leadership.
Jibrin wanda bai gajiya da a zarge-zargen da ya ke yiwa shugabancin majalisar ba, ya dora alhakkin matsalolin siyasa da na zamantakewa da kuma na tattalin arzikin kasar nan da samun tushe daga majalisar, sannan ya cigaba da cewa, Kakakin Majalisar Dogara ya aka zaba a shekarar 2007 ya karbi kimanin Naira biliyan 1 da miliyan 5.
KU KARANTA: Na fi karfin EFCC ta bincike ni –Yakubu Dogara
Sannan mataimakin Kakakin majalisa da Shugaban masu rinjaye Gbajabiamilla, da mai tsawatarwa a majalisar, kawo yanzu sun karbi biliyan 1 da milyan 2, kuma da miliyan 800 kowannensu, haka ma sauran kamar haka;
“Mataimakin mai tsawatarwa Pally Iriase da ke majalisar tun shekara ta 2011, zuwa yanzu ya karbi Naira miliyan 700. Shugaban marasa rinjaye Leo Ogor wanda ke majalisar tun shekara ta 2011 ya karbi Miliyan 700, mai tsawatarwa marasa rinjaye Binta wacce ta ke majalisar tun shekara ta 2011 ta karbi miliyan 700.”
Jibrin Kofa ya kuma kara da cewa “…Wadannan shugabannin majalisa su 10 sun lankwame kimanin Naira biliyan 10 ba kuma shi ke nan ba, kuma yawancin kudaden nan an karkatar da su ne ta hanyar zuwa wasu abubuwa na kashin kai, a maimakon ayyukan majalisa”.
The post Shugabannin Majalisa sun lankwame biliyan 10 –Jibrin appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read Naij.com 24/7.
Post A Comment:
0 comments:
We’re eager to see your comment. However, Please keep in mind that all comments are moderated according to our Comment Policy and all the links are nofollow. Using keywords in the name field area is forbidden.
Comment Using Either Disqus or Default Comment Mode.