‘Yan arewa sun iya daukar wanka a cewar Temitope Popoola ta Naij.com, don haka ta zabo wasu samari ‘yan kwalisa da suka dau wakan colabo da suwaga har da ma da na fitted cikin har da wasu ‘yan fina-finan Hausa.
Muna gabatar muku da wasu samari ‘yan kwalisa daga arewacin kasarnan daga tsatson Hausa Fulani, don ku sani cewa ba duk wanda ku ka hadu da shi a kudu yana aikin wahala ko na kaskanci ba, ku dauke shi a matsayin baya ga dangi a Najeriya.
Adam A Zango: mawaki mai shiryawa da kuma fitowa a fina-finan Hausa
Adam A Zango: Mawaki mai shiryawa da kuma fitowa a finan Hausa, fina-finansa da wakokinsa na jan hankali masu kallo musamman matasa. Ya taba janyo ka-ce-na-ce a tsakanin matasa sakamakon wani furuci da yayi na cewa yafi matasan wata jiha a arewa iya daukar wanka, wanda hakan ya sa suka yi caaa a kansa, ko hakan ta tabbata ke nan da sa dan wasan a jerin matasa ‘yan kwalisa daga arewa na Naij.com?
Yakubu Mohammed ko Mallam Yax
Yakubu Mohammed: Na hannun daman Sani Danja, kuma Mawaki, mai shiryawa da fitowa a fina-finan Hausa, Malam Yax kamar yadda ake kiransa, yanzu za a ce ya karkata ga fitowa a fina-finan da ke yi a kudancin kasar watau Nollywood, bayan ga fitowa a salon wakokin na zamani da ‘yan kudun. Dan asalin jihar Plato, shi ya lashe kyautar jarumin jarumai daga Arewa na City People Entertainment award na shekarar 2015.
Misra Yax da kyautarsa ta City People
KU KARANTA: Hana fim village a Kano kwangilar malamai ce
SadiqSani Sadiq daya daga cikin taurarin fina-finan hausa
Sadig Sani Sadiq: Jarumin jarumai na Kannywood Awards da shima ya cinye a wannan shiga na zabi ki darje daga arewa
The post Zabi ki darje ‘yan kwalisa daga arewa (Hotuna) appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read Naij.com 24/7.
Post A Comment:
0 comments:
We’re eager to see your comment. However, Please keep in mind that all comments are moderated according to our Comment Policy and all the links are nofollow. Using keywords in the name field area is forbidden.
Comment Using Either Disqus or Default Comment Mode.